Nan ba da jimawa ba zamu hana shigo da Kifi da Madara cikin Najeriya – Sabo Nanono

0
2336

Ministan noma na ƙasa Sabo Nanono, ya bayyana ƙudurin gwamnatin tarayya na hana shigo da Kifi da Madara cikin ƙasar nan.

Minista Sabo Nanono, ya bayyana hakan a lokacin da ya ke jawabi a gurin wani taro da aka gudanar a gwamnatin tarayya da ke birnin Dutse da ke jihar Jigawa.

Haka kuma Sabo Nanono ya ce gwamnatin tarayya za ta sake yin nazari akan nau’ikan abincin da ake shigowa da su cikin ƙasar nan, domin Najeriya ƙasa ce da Allah ya albarkaceta da tarin albarkaru, wanda hakan ke alamta cewa babu wani abu da ba za a iya samar da shi a cikin ƙasar nan ba.

Hakazalika, Sabo Nanono ya ce akwai kimanin shanu guda miliyan 25 a faɗin Najeriya, sai dai matsalar ita ce har yanzu ba a san yadda za samu isasshiyar madara daga gare su ba.

Ya ce tuni gwamnatin tarayya ta fara samar da ƙananan masana’antu da za su dinga sarrafa madara, wanda hakan zai rage shigo da madara cikin ƙasar nan.

A ƙarshe ya ce sun buɗe irin wannan masana’antar ta samar da Madara a ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu da ke jihar Kano, wanda fulani masu yawa su ke amfana da wanna n tsari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here