Ni ɗan kallo ne, ban san halin da jam’iyyar APC ta ke ciki ba – Rotimi Amaechi

0
11283

Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa bai san halin cukumurdar rikicin da jam’iyyar su ta APC ke ciki ba.

Jam’iyyar APC dai ta rufta cikin rikici, tun bayan da Babbar Kotun Daukaka Kara ta jaddada dakatarwar da shugabannin jam’iyyar APC na Mazabar Adams Oshiomhole su ka yi masa.

Bayan nan sai bangarori biyu suka fito su na irikrarin shugabancin rikon jam’iyyar.

Akwai bangaren Kwamitin Gudanarwa na Kasa wanda suka ce tsohon gwamnan Oyo, Abiola Ajimobi ne Shugaban Rikon Kwarya.

Sai kuma kamar daga sama Mataimakin Sakataren Jam’iyya na Kasa, Victor Giadom ya fito ya ce shi ne Shugaban Rikon Kwarya halastacce.

Giadom dai na daya daga cikin ‘yan gidan siyasar Rotimi Amaechi, wanda ke adawa da bangaren Bola Tinubu, kuma ba ya goyon bayan takarar Shugabancin Kasa da Tinubu aka ce zai nema a 2023.

APC ta kara rincabewa da kacamewa bayan a ranar Laraba, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya na bayan bangaren shugabancin Giadom, ba na Ajimobi ba.

Yayin da duk ake wannan kacakauran rikici kuwa, shi Ajimobi ya na gadon asibiti, ya na jiyya mutu-kwakwai-rai-kwakwai.

Giadom ya kira taro, wanda Buhari ya sanar cewa zai halarta ta hanyar halartar taron zamani saga gida.

Rikicin na APC wanda aka hakkake cewa daga Jihar Rivers da Edo ake kitsa shi, ya samo asali ne daga rikicin Obaseki da Oshiomhole.

Dangane da abin da ke faruwa ne Amaechi ya ce, “ni ban san komai da ke faruwa na a yanzu a cikin jam’iyyar APC.

“Kowa ya san ni sarai idan ina da abin da zan yi magana a kai, to na kan yi. To amma tun bayan 2015 na sha cewa akwai gyara a tafiyar nan fa. Kenan a yanzu babu abin da zan fadi wanda ban fadi ba a baya.”

Da aka tambayi Amaechi batun wasu matasa da suka yi kurarin za su babbake jihar Rivers idan wani abu ya samu shi Amaechi din, sai ya ce, “duk wanda ya san ni a baya da yanzu, ya san ni karya doka da oda ba hali na ba ne.

“Ni ban ma tsaya a kan bin doka da oda kadai ba. Ni mutum ne mai tsoron doka matuka.”

Ya ce mai tsoron doka kuwa ba zai daure wa wasu gind in su fita su karya doka ba.

Premium Times

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here