Nijeriya Ta Kwaso ‘Yan Kasarta 360 Daga Dubai Da Pakistan

0
81

Gwamnatin tarayya a ranar Juma’a ta yi nasarar kwaso ‘yan kasarta 300 wadanda suka kasa dawo wa daga Dubai, tare da kuma wadansu ‘yan Nijeriyar 56 daga kasar Pakistan cikinsu kuwa harda ‘yan Pakistan din guda hudu.

Ministan harkokin wajen Nijeriya, Geoffrey Onyeama shi ne ya bayyana hakan a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a @GeoffreyOnyeama.

“A karshe dai mun yi nasarar kwashe ‘yan Nijeriya 56 da kuma ‘yan Pakistan guda 4 daga birnin Islamabad zuwa Abuja a jirgin kamfanin TARCO AVIATION Co. Ltd.” Inji shi.

Ya kara da cewa; “Jirgin Emirates na UAE shi kuma ya dauko ‘yan Nijeriya 300 wanda ake sa ran zai sauka da karfe 3.55 na yamma daga Dubai.” Inji Onyeama.

Sai dai ya ce wadanda suka dawo za a tabbata da an bincikensu cikin awa 72, sannan a killace su na tsawon mako biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here