Obasanjo ya bukaci Buhari da ya hana jami’an tsaro kisan masu zanga-zanga

0
157

Tsohon Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dakatar da sojoji da kuma sauran jami’an tsaro daga amfani da karfin da ya wuce kima akan masu zanga zanga.

A sanarwar da ya rabawa manema labarai, Obasanjo ya bi sahun fitattun shugabannin duniya irin su tsohon mataimakin shugaban Amurka Joe Biden da tsohuwar Sakatariyar harkokin waje Hillary Clinton wajen Allah wadai da yadda sojojin suka afkawa masu zanga zangar.

Yayin da ya bukaci masu zanga zangar su kai zuciya nesa ya kuma bukaci gwamnati da tayi Nazari kan bukatun su wadanda yake cewa abubuwa ne masu yiwuwa.

Gwamnan Lagos Babajide Sanwo Olu yace babu wanda ya mutu a harbin da sojoji suka yi jiya, sai dai wasu mutane sun samu raunuka kuma ya ziyarce su a asibiti.

 

Rfi Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here