Ra’ayi: Ƴancin Kai A Najeriya; Jiya Alhamis Yau Alhamis ba ta sauya zani ba

0
333

Ɗaya ga watan Oktoba shekara ta dubu ɗaya da ɗari tara da sittin.

Tun muna makarantar firamare ake biya mana wannan shekarar muna haddacewa, ko baka haddace don matsayin ta na shekarar da ƙasar ka Najeriya ta samu yancin kai ba zaka haddace don gudin faɗuwa jarrabawa idan kaci karo da tambaya makamancin haka.

Ko da yake dai bani da cikakken sanin lokacin da Turawan mulkin mallaka suka wanzar da nasu murkin akan Al’ummar mu, amma dai tarihi ya bayyana mana yadda aka dinga cikinin bayi a wancan ƙarnin, ta yadda turawa ke shigowa da kayayyaki suna musayar su da bayi, wanda shuwagabannin al’ummar wuraren ne kaɗai ke mu’amala da su kuma su ribantuwa da cinikin.

Abin kam ba daɗi, amma dai komai mai mucewa ne bisa iko da hukuncin Ubangiji.

 

Alhamdulillah!

Gashi dai wancan ƙarnin ya wuce sai dai kuma Jiya Alhamis Yau Alhamis bata sauya zani ba. Mun fita daga hannun turawan da suka yi mulkin mallaka mun koma hannun ƴan’uwan mu suna nasu mulkin ƙarfa-ƙarfan suna kuma cin karansu babu babbaka.

Masha Allahu an samu yancin kai musamman a bangaren faɗin albarkacin baki duk da dai shima ana shirin yi masa hawan ƙawara ta hanyar sauya salo da cusawa masu faɗin ra’ayin su musamman wanda ya ci karo da na gwamnati tsoro domin su kasa sukar ta.

Ana girma ana daɗa susucewa abin sam babu armashi.

Shekaru sittin fa ba kwana sittin bane, tafiya ta miƙa, yana da kyau dai idan an girma asan an girma.

TSARO

Babu wani yanci ga al’ummar da take cikin ɗar-ɗar, zullumin, fargaba da tsoro saboda barazanar abinda rashin tsaro kan iya haifarwa a koda yaushe.

RASHAWA

Babu wani yanci ga ƙasar da cin hanci, rashawa, almundahana ya zama abin ƙawa ba ga shugabannin ba baga talakawa ba.

TATTALIN ARZIKI

Yancin dai har yanzu bai kai yanci ba tunda har yanzu talaka yana cikin ƙuncin rayuwa, matsi, yunwa da fatara.

ILIMI

Ina wani yanci ga ƙasar da karatun ɗan talaka yake taltalbatalti ya gagara ingantuwa saboda son Zuciya na wasu daga cikin shuwagabannin ta.

LAFIYA

Ina yancin yake a bangaren lafiya ? Tambayar da zaka fara yiwa kanka kenan yayin da ka shiga wasu asibitocin gwamnati, saboda rashin kayan aiki, rashin inganta muhalli da ma rashin isassun ma’aikata.

A matsayin ka na talaka bazaka gane ihun banza kake yi na samun yanci kai ba sai ka kai matarka, ƙanwarka, ko yayarka asibiti haihuwa da daddare ance ka siyo kyandir da maganin sauro da zatayi amfani dashi.

Safar hannu da za’asa a dubanta ma sai ka siya.

LANTARKI

Wai har wani ihun yanci ake yi a kasar da har yanzu wani talakan bai san ɗadin wutar lantarki ba ballantana yasan amfanin ta gareshi?

Har yanzu akwai fa ƙauyukan da ba sa ganin haske sai tarin wayoyi na yaudara marasa amfani.

Matsalar bata shuwagabanni ko masu arzikin cikin mu bane kawai, mu ma talakawa muna da namu.

Sai mun haɗu mun gyara, mun yarda muna son cigaban junan mu, mun haɗe kawunan mu, mun cire son Zuciya, hassada, ƙyashi, bakin ciki, handama da kuma babakere akan duk wata dama da muka samu, mun kuma daina yunkurin taɗe duk wani yunkurin cigaban Alkhairi da wani ya samu.

Domin idan wani ya samu wata dama ta cigaba da take ƙarƙashin ikonka, ka jawo wuyanshi ta baya kuma kasa ƙafa ta taɗe shi har ya gagara samun wannan damar to zai saka wannan a ransa, idan har ya samu wata Damar shima bazai tausayawa bayan ka ba, matsalar ba a bayan ka da bayan bayanka kawai zata tsaya ba, sai ta tsallaƙa ta shafi bayan wasu, to me akayi kenan? haba! kai kaɗai ka haddasawa dankwafewar dubban mutane saboda hassada da son zuciyarka.

Ya kamata mu gyara zuƙantan mu, idan muka gyara tun daga ƙasa to saman ma dole su gyara tunda mune Su, suma kuma sune mu.

Idan babu al’umma to tabbas babu shugabanci, kamar yadda idan babu shugabanci babu Al’umma.

Allah ka raya Nageriya ka Albarkace ta, ka wadata jama’ar cikin ta da hankali, nutsuwa, hangen nesa da kuma tausayawa juna.

 

Hauwa Shehu marubuciya ce kuma mai yin sharhi akan al’amuran yau da kullum, ta rubuto daga Kano. 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here