Ra’ayi: Dole sai an yi yaƙi da abubuwa biyu idan ana son gyaran tarbiyya

0
3037

Akwai abubuwa da yawa da ke damuna amma akwai guda biyu da suke taka rawar gani wajen ɓata tarbiyya yara mata da matan gabaki daya, wanda lalle sai mun saka ido akan su idan muna so mu bayar da kariya daga cin zarafin mata da ake da kuma bata masu tarbiyya.

Sai mun tashi tsaye mun yaki bokaye da malaman tsibbu wanda duk wannan bala’in fyade su suke koyawa mutane su ce idan sun yi za su yi kudi, sannan kuma Allah kadai ya san matan auren da suke lalata da su idan sun je wajensu neman ayi masu magani, da wanda suke ko ya masu su nemi matan su ta hanyar da bai dace ba ko lokacin da suke jinin al’adarsu da abubuwa makamanta irin haka da suka sabawa dabi’a.

Sannan sai mutane masu fakewa da su na Allah ne ko su fake da sunan son Annabi kuma mutane su ke sakin jiki dasu wanda daga karshe za ka samu suna lalata da ƴaƴa matan da suke koyarwa.

Irin wannan nau’in mutane ba zaka gane illar da sukayi wa al’umma ba sai sanda aka bincika za ka ga mafi yawan irin wannan mutane suna dauke da cuta..

Ƙaddara matar aure taje sun saka mata cuta itama taje ta sakawa mijinta in yana da wasu mata suma duk ya goga masu, haka kuma idan budurwa sun lalata rayuwarta wata daga ranar da tasan namiji ba zata iya kame kanta ba, shi ke nan ta fara zina kaga sun sakata a hanyar karuwanci sun kuma mayar da ita kamar kasuwarsu sai yadda suka yi da ita suna biyan bukatarsu.

Ba wanda ba ya zunubi amma abinda yasa ake hana shi shi ne za ka ga duk zunubi akwai wani abu na cutarwa ne ga mutum shi kan kansa shiyasa a zunubi da yake mutum na shi kadai ne kullum addini abinda baya so shine bayyana wa dan kar wani ya gani ya koya kullum shi zunubi da laifi irin wannan ana hanashi ne saboda cutarwa da zai yi ga al’umma.

A karshe lalle muna shawarta al’umma da su saka ido akan irin wananan mutane kuma kar dan mutum yana da’awar malanta ko yana nuna shi mai addini ne a saki jiki dashi a barshi yayi abinda yaga dama, dole ko karatu ne mata ke koya wajensa iyaye su saka ido ya zamana akwai tsari kuma a dinga daukar mataki mai tsauri wanda in mutum ko iskanci zai yi yayi shi aka karan kansa amma ba a dinga shiga rigar addini ana bata masa suna. Sannan kuma dole a matsa wajen gwajin jini kafin ayi aure sabida abunda zai je ya zo.

 

Kassim Tijjani Turaki Dan Jarida Ne kuma Mai Yin Sharhi Akan Al’amuran Yau Da Kullum, Ya Rubuto Daga Kano

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here