Ra’ayi: Gwamnatin Zamfara Ba Mu Yafe Ba – Aisar Musa Fagge

0
5246

Wai mutumin (Femi Fani Kayode) da ya ce za su yi bikin jefa Qur’ani a Tekun Fasha shi ne yau Masauratar Shinkafi za su ba shi sarautar “Sadaukin Shinkafi.” Sadaukin kare su wa? Talakawan da y’an bindiga suke kashewa ko kuma wad’anda ake kashewa idan sun je Kudancin ‘Kasar nan Cirani? Wai don Allah wa ya tsine mana ne? Wane bakin uwa ne ki bibiyarmu?

Duk wani mutum mai daraja a Arewa babu wanda FFK bai ci mutuncinsa ba. A duniya a yau babu wanda ya tsana irin Musulmai, Arewa, Hausa-Fulani. A last year da aka yiwa Musulmi kisan wulaqanci a Ile-Ife, jihar Osun FFK fitowa yayi ya ce laifin Musulmai ne. Kuma duk rikicin da aka tsakanin manoma da makiyaya FFK cewa yake Fulani ne kuma tsohuwar agenda ce ta Jihadin Dan Fodio da yunqurin Musuluntar da Nigeria.

Abun da zai ba ka mamaki, a y’an siyasar jihar Osun shi d’in ba kowa bane. Kawai an d’auke shi a matsayin d’an iska mai zage-zage a kafafen sada zumunta. Amma mutanenmu suka maida shi wani gunkin da dole su ke buqatar zage-zagenshi a duk lokacin da aka kad’i kugen siyasa.

Gwamnatin Jihar Zamfara da Masarautar garin Shinkafi su sani cewa sun ci mutuncin Musulman Nigeria ba wai Hausa-Fulani kad’ai ba. Kuma yanzu sauran qabilun qasar nan za su qara tabbatarwa mu d’in banzaye ne, shashashai ne, wawaye ne, mutane ne da ba su san ciwon kan su ba. A lokacin da kullum shafukanmu suke ta kira a kawowa jihar Zamfara d’auki daga ta’addanci y’an bindiga, a lokacin ne ita kuma gwamnatin jihar ta ga ya kamata ta saka mana da bawa maqiyinmu sarautar gargajiyar da kullum yake suka.

Muna kira da malamanmu da su yi khud’ubobin Juma’ah akan gwamnatin Jihar Zamfara bisa wannan rashin mutuncin da ta yi mana. A yiwa gwamnatin da masarautar bulala sosai yadda za su dawo hayyacinsu su gaggauta cirewa wannan matsiyacin ARNEN rawanin da suka nad’a masa. Wannan baqin tarihin da kuka rubuta tarihi ba zai manta da shi ba. Da za a tashi Sir Ahmadu Bello Sardauna a kabarinsa a nuna masa faifan videon nad’in sarautar nan wallahi na tabbata Gamji ‘Dan Kwarai sai ya tsinewa wad’anda suka kawo wannan tunanin albarka saboda cin amanar Arewa da suka yi.

 

Allah  ya isa!

Daga shafin Aisar Fagge.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here