Ra’ayi: Maryam Yahaya ba ta da mutunci – Aliyu Dahiru Aliyu

4
21063

Wallahi Allah Maryam Yahaya bata da mutunci. Ya mutum zai yi tattaki tun daga Yobe ya zo ganinki amma ki ki saurarsa? Wannan ai hauka ne da rashin sanin mutuncin masoyi. A ce saboda sonki har fiya-fiya bawan Allah ya sha amma ko a kula ta gagara?!

Idan yanzu kin ga kina tashe to ki tambayi yau ina Safiya Musa? Ina Fati Muhammed? Ko Mansura Isah da ta auri Sani Danja ina take yanzu? Ban da ma tana aiyukan tallafi wa zai tuno da labarinta? Su Hadiza Kabara kuwa yanzu rara-gefe suke. Duk wadannan an so su fiye da ke.

Yan wasan Hausan nan ku dauki kanku ku wani aza girman kan banza da wofi. Haka na ga wani mun shiga rastuwarent a Abuja yana ta wani kobarewa sai ka ce wata tsiya zai yi a gurin. Ke fa ba wani ilimi ne da ke na yabawa ba. Kudin ma wallahi babu. Sai dai hoto a Instagram da dan karan girman kan banza da wofi. In banda ma tuwo ya cika idon yaron ni sai na rasa me ya baro a Yobe ya tafi Kano kallon wannan yarinyar!

Shi masoyinka ai naka ne ko daga wani kauye yazo. Kin ganni nan wallahi zan iya haduwa da Messi ko Ronaldo ya yi gaba na yi gaba don basu dameni ba. Amma da muka hadu da Ali Nuhu a jirgi na ga mutane sun shareshi sai da na taso muka tattauna ko don na tuna masa shi “celebrity” ne da bai kamata a nuna masa bai isa ba. To bai kamata kuma idan kun shiga cikin jama’a ku dinga wulakanta wadanda suke nuna kun i sa ba.

Daga Shafin Aliyu Dahiru Aliyu

4 COMMENTS

  1. Comment:gaskiya wannan bai kamata ba,koda shima baisan me yake bane dun mai hankali baxai tashi takanas ta kano wai yaje ganin yar film ba!

  2. Suma wawayen da suke mutuwa akan yan Hausa film maganin su wallahi ban ga abun Burgewa ba mutane jahila barin su Maryam yahaya ma kauyawan banza da wofi. Mchww

  3. Gaskiya ina ga Mal. Aliyu Dahiru ya kwafsa a nan. Malamin ya manta cewa na farko Maryam ba ta san mutumin nan ba. Na biyu bai shaida mata kafin ya zo ba, maana bai sami appointment ba. Na uku a zamanin nan ai ganin kowa karazube yana da hadari.
    Ni ina ganin matashin nan da ire-irensa ya kamata a zarga, a kuma nuna musu muhimmancin rai. Ran nan fa ba namu ba ne, na Allah ne. Don me saboda a rashin wani abu da muke so, zai sa mutum ya kashe kansa? Wannan ai butulci ne ga Allah. Ya kamata mu tunatar da matasanmu cewa duk wanda ya kashe kansa fa wuta zai ci bal bal bal!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here