Ra’ayi: Matasa akwai babban ƙalubale a gaban mu

0
400

Matasa mune ƴan shaye-shaye, mune ƴan zaman banza, mune muka ƙware wajen cin mutuncin junanmu, mune ƴan social media campaign ga ƴan siyasa, mune ƴan rally ga ƴan siyasa, mune ƴan sara suka, mune ƴan jagaliya, sannan da yawa daga cikinmu ko kaɗan bamu san ciwon kanmu ba.

A zahiri mun san cewa babu wani tanadi ko kuma wani gagarumin shiri da shuagabannin mu suke yi mana domin gyaran rayuwar gobenmu, sai dai ma tauye mana haƙƙin mu da kuma sama da faɗi da dukiyarmu da wasu daga cikinsu sukeyi, bayan kuma duk wata gwagwarmayar siyasa da kuma cigaban dimokuraɗiyya 70% mu matasa mune muke bada gudunmawa wajen tabbatuwar hakan.

Matasa mun sani cewa ko tallafi da Gwamnati take ta ikrarin tana bayarwa ga matasa akoda yaushe, ko kaɗan baya isowa wajen da yawa daga cikin matasan, saboda wasu masu baki da maiƙo sune suke haɗiye komai ba tare da tunanin cewa Allah (S.W.T) zai tambayesu akan hakan ba.

Ƴan’uwana matasa mu sani cewa tabbas akwai babban ƙalubale a gabanmu wanda ya kamata mu tashi tsaye mu yiwa kanmu karatun ta nutsu, mu ajiye duk wata jagaliyar siyasa da sauran duk wasu munanan ɗabi’u da halaye namu, mu maida social media wajen tattauna matsalolin mu tare da neman mafita akan yanda zamu magance duk matsalolin da suka addabemu, ba wai mu maida social media dandalin cin mutuncin junanmu da kuma jagaliyar siyasa ba.

Ina roƙon Allah (S.W.T) Ya taimaki rayuwarmu mu matasa, ya kuma kawo mana shiriya da gyara acikin rayuwar mu.

Adamu Kazaure (Ɗan Almajiri) ya rubuto daga Kano 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here