Ran Maza Ya Ɓaci: Tsoffin sojoji sun buƙaci a basu damar komawa daji yaƙar Boko Haram

0
558

Wasu daga cikin tsofaffin sojoji a jihar Kano sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya basu dama su sanya kaki su kuma dau bindiga domin yaki da ‘yan Boko Haram.

Tsofaffin sojojin da akalla shekarunsu ya tasamma 70 zuwa 80 sun ce duk da yawan shekarun da suke dashi matukar aka basu dama, to za su kawo karshen matsalar tsaro a arewacin kasar nan.

Guda daga cikin mazan jiyan mai mukamin manjo Adam Umar Usman ya ce har yanzu suna da kishin kasar nan kuma suna takaici a duk lokacin da wani soja ya rasa ransa a fagen fama.

Ya ce a kwai manyan sojoji dake kara ta azzara yakin Boko Haram da basa son zaman lafiya a kasar nan.

“Su kiramu mukoma dajin, bama tsoron mutuwa domin tana kan kowa,” a cewar sa.

Shima wani daga cikin tsofaffin Sojojin mai suna Ali Galadima, cewa yayi nasa tsoron yaki da Boko.

A cewarsa mafiya yawan sojojin da ke yaki da yan ta’addar a yanzu basu da gaskiya, domin sukan fitar da sirrin aikinsu ga abokan gaba.

Ya ce yakamata a dinga yin bincike sosai kafin daukar kowanne mutum aikin soja.

Yana mai cewa matukar za a dinga daukar aikin soja ba tare da yin kwakkwaran bincike ba to tabbas yakin Boko Haram ba zai kare ba.

Kano Focus

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here