Ranar Arewa: Arewa Da Sauran Gyara – Hauwa Shehu

1
4115

Sakina da Azima su biyu ne zaune a falon amma tsit kake ji kamar ba kowa, kowacce ta harɗe a kan kujera tana faman lallatsa wayarta.

Idan ka nazarci fuskokin su zaka fuskanci ɗaya na cikin nishaɗi da annasuwa yayin da take latsa wayarta, a bangare guda kuma, ɗayar damuwa da takaici ne ƙarara shimfiɗe akan fuskanta.

Cikin murmushi Azima ta ɗago kai ta kalli yar’uwarta sannan tace ” yar’uwa yau ban ji ɗuriyarki a social media ba, bayan kuma yau ranar mu ce.

Kallon rashin fahimtar inda zancen ya dosa Sakina tayi mata.

“Ranarku? Ku suwa ke nan?

Mu yan’ arewa mana, ba ki ga yadda ake ta trending a Twitter ba ? Facebook da Instagram ana ta amfani da #tag wajen nuna farin ciki ga wannan rana wacce aka yiwa laƙabi da 1st Arewa day.

Nima yanzu kokari nake in yi editing video da images in makasu a dukkannin handle dina na social media, ya zama Dole muyi murnar domin ranar muce.

Azima ta ƙara faɗaɗa murmushinta sannan ta kara dacewa ” kema yana da kyau kiyi haka, domin mafi yawancin followers dinki yan arewa ne, yana da kyau ki ƙara musu ƙaimi da kuma dalilin da zai sa su ci gaba da binki.

Hmmm..! Sakina ta saki wata nannauyar ajiyar zuciya sannan ta tattara nutsuwarta ga Azima kafin da fara da cewa.

“Bana kalubalantar murnar ranar arewa, da ace arewar da na sani kuma nake jin labarin ta a da ita ce har yanzu to da nafi kowa caraɗi a kafafen sada zumunta, ke harma da zahiri.

“Arewarmu ta yanzu fa, na fuskantar mummunan kalubale wajen zaman lafiya, ilimi, tattalin arziki, kwanciyar hankali, zumunci da kuma kyakkyawan shugabanci, saɓanin arewarmu ta da, da duk ta tara wadanda darajojin.

A ganina ba yanzu ne lokacin murnar ranar arewa ba, domin Arewa da sauran gyara har yanzu, abinda Arewa tafi buƙata yanzu shi ne:

1. Addu’a daga majibinta yankin dama al’umma baki daya.

2. Adalci daga shuwagabannin mu.

3. Jajircewa, dogaro da kai da sanin ciwon kai daga matasan mu.

Ya zama dole mufarka daga nannauyan baccin da mu ke yi, musan menene yancin mu, mutuncin mu, martabar yankin mu, da kuma abin da ya kamata muyi domin dawo da martaba, zaman lafiya, tattalin arziki, da kwanciyar hankalin da da can aka san arewa dashi.

Daga lokacin da mukasan kanmu daga lokacin shuwagabannin mu suma zasu fahimci abin da ya kamata suyi.

Sakina na kaiwa nan a bayaninta, ta kai dubanta ga Azima wacce jikinta yayi sanyi.

Ina fatan dai kin gama editing ɗin video da images din da zakiyi zuba a shafukan ki na sada zumunta domin mabiyanki yan arewa?

Cikin sanyin jiki Azima tace ” Babu bukatar haka yanzu ai, na gamsu da hujjojin ki tabbas arewa akwai gyara.

Kin ga abin da na rubuta a shafina, ta ɗago wayarta tana nuna wa sakina.

Idon sakina ya kai kan rubutun da tayi da manyan baƙi.

ALLAH KA CECI YANKIN MU NA AREWA KA DAUWAMAR MANA DA ZAMAN LFY DA KWANCIYAR HANKALI.🙏🙏🙏

Hauwa Shehu Marubuciya Ce Kuma Mai Yin Sharhi Akan Al’amuran Yau da Kullum, Ta Rubuto Daga Kano.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here