Ranar matasa ta duniya: Wanne ƙalubale matasan Najeriya ke fuskanta?

0
1409

A yau ne ake bikin ranar matasa ta duniya, an dai ware wannan ranar ne dai domin baiwa gwamnatoci dama su janyo hankulan jama’a kan batutuwa da suka shafi matasa.

Majalisar Dinkin Duniya, ta ware duk ranar 12 ga watan Agusta a matsayin ranar matasa, don duba ga matsaloli da kuma hanyoyin warware su a fadin Duniya.

Babbar matsalar da ke damun matasan dai ba ta wuce rashin samun aiyukan yi ba, wanda suke nemi shugabanni da su tashi tsaye wajen samar da ayyukan yi da zasu basu damar samun rayuwa mai inganci.

A wannan zamani dai wasu ‘yan siyasa na amfani da matasan wajen basu kudi da tsunduma su cikin bangar siyasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here