Rarraba Najeriya shiya-shiya ne mafita kawai a halin da ake ciki – Balarabe Musa

0
269

Tsohon gwamnan jihar kaduna, Balarabe Musa ya bayyana cewar raba kasar nan zuwa yanki 6 shine kawai zai kawo dauwamammen zaman lafiya da hadin kan ‘yan kasar.

Balarabe Musa ya bayyana hakan ne yayin zantawa da Wakilin Jaridar the sun. Inda ya bayyana kiraye kirayen da kungiyoyi da wasu ‘yan siyasa keyi na sauya fasalain tsarin gudanar da kasar a matsayin abinda bai zama dole ya haifar da cigaba ba da hadin kan kasar ba.

Amma idan aka maida kasar yanki 6 ko 7, hakan zai kawo cigaban kasar da hadin kanta. Ko a lokacin baya da ake tafiyar da kasar a irin wannan tsari an samu cigaba sosai fiye da wanda muke gani a halin yanzu.

Inda za a tafiyar da tsarin kowani fanni na kasar nada wakili hatta matsalar tsaro, talauci, da rashin aiki duk zai ragu. Domin Wannan tsarin da ake kai yanzu babu abinda ya haifar wa kasar illa almundahanar kudaden gwamnati, da kuma satar dukiyar kasa. Shugaban kasa da ya fito daga arewa babu abinda ya tsinanawa arewa domin hatta mahaifar sa katsina babu zaman lafiya balle sauran yankin kasar kamar yadda Balarabe Musa ya bayyana”

Jam’iyyun PDP da APC duk sun gaza wurin kawowa kasar nan cigaba, kuma sunfi son a tafi a irin wannan tsari na jam’iyyu biyu kachal wanda hakan ba zai haifarwa dimokaradiyyar kasar wani cigaba ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here