Rashin Girmama Al’adu Ke Kawo Yawaitar Fyade –Tsohon Minista

0
163

Cif Ndueso Essien, tsohon Ministan gidaje da ci gaban birane, ya bayyana cewa watsar da al’adu ya taimaka matuka wajen yaduwar fyade.

Essien ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a yayin da wadansu mata suka yi zanga-zanga kan yawaitar fyade da cin zarafin mata da ya gudana a karamar hukumar Eket na jihar Akwa Ibom.

Tsohon ministan ya ce; mafi yawan ‘yan Nijeriya sun watsar da al’adunsu, a yayin da wadansu iyalan ma ba su damu da ‘ya’yansu ba, musamman ‘ya’ya mata.

Inda ya shawarci Iyaye da su bai wa ‘ya’yansu kulawa ta musamman, inda ya ce domin yara na bukatar a ba su kulawa da ilimi.

Sai dai kuma ya yi Allah-wadai da yawaitar fyade da masu fyaden tare da wadanda suke cin zarafin mata a fadin kasarnan. Sannan ya nemi da a rika hukunta masu aikata fyaden.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here