Rikicin Jam’iyyar APCn Jihar Kano: Akwai Yiwuwar Samun Sarakuna Biyu A Gari Ɗaya

0
499

DAGA Bashir Abdullahi El-Bash

-Yau Jam’iyyar APC A Jihar Kano Ta Faɗa Cikin Irin Rikicin Cikin Gidan Da Jam’iyyar CPC Mai Alƙalami Ta Shugaba Ƙasa Muhammadu Buhari ta fuskanta a shekarar 2011, Rigingimun Da Su Ne Su Ka Ɓarar Mata Da Garin Dafa Tuwo A Jihohi Da Dama Na Wannan Ƙasa.

-Yau An Fita Fagen Zaɓen Shugabannin Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Gwamna Ganduje Ya Fita Da Ɗan Takararsa, Alhaji Abdullahi Abbas Ɗan Sarki, A Kuma Hannu Ɗayau Su Ma Ayarin Sanata Ibrahim Shekarau Sun Fita Da Nasu Ɗan Takarar, Wato, Alhaji Haruna Zago.

-Idan Aka Yi Shugaban Jam’iyya Biyu A Jam’iyya Ɗaya, Idan An Zo Batun Fitar Ƴan Takara Na Ƴan Majalissun Tarayya Da Na Jihohi Da Kujerar Gwamna, To Kowane Tsagi Za Su Fitar da Nasu Ƴan takarkarun, Hatta Batun Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ma, Kowane Tsagi Za Su Bi Wanda Duk Su Ka Ga Dama, Daga Nan Kuma Kotu Za A Koma A Cigaba Da Fafatawa Ko Dai Wani Tsagin Ya Yi Nasara Ko Kuma Duk Su Rasa.

Yau Asabar, 16 ga watan Oktoba, 2021.
Rikita-rikitar siyasa ta na cigaba da yaɗuwa a cikin jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Kano da ƙasa baki ɗaya. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ja dunga tare da tawagarsa, su ma manyan jiga-jigan ƴan siyasa na jam’iyyar ta APC bisa jagorancin tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau da Attajiran Jihar Kano da Malamai da ƴan kasuwa, da ƴan Boko, Matasa su ma sun ja tasu dungar sun kafe akan aniyarsu ta nemowa Jihar Kano da APC kykkyawar makoma kafin zaɓen 2023.

Yau an fita fagen zaɓen shugabannin jam’iyyar APC na Jiha, gwamna Ganduje ya fita da ɗan takararsa, wanda kuma shi ne shugaban jam’iyyar mai ci, Alhaji Abdullahi Abbas Ɗan Sarki. A kuma hannu ɗaya su ma ayarin Sanata Ibrahim Shekarau sun fita da nasu ɗan takarar wato Alhaji Haruna Zago.

Abin da zai faru daga ƙarshen lamarin shi ne samar da sarakuna biyu a gari ɗaya, ma’ana: ɓangaren gwamna Ganduje za su bayyana shugaban jam’iyya, haka zalika su ma tsagin Sanata Malam Ibrahim Shekarau za su bayyana shugaban jam’iyya duk a jam’iyya ɗaya wato (APC).

Idan hakan ta faru, an buɗewa jam’iyyar babban ramin cigaba da samun hayaniyar siyasa da matsalolin da za su iya kaita ga rasa Jihar Kano a babban zaɓen da ke tafe na shekarar 2023. Domin matsalar ita ce, idan an zo batun fitardda ƴan takara na ƴan majalissun tarayya da na Jiha da kujerar gwamna, to kowane tsagi za su fitar da nasu ƴan takarkarun, hatta batun takarar shugaban ƙasa, kowane tsagi za su bi wanda duk su ka ga dama.

Kusan abin da doka ta tanadar akan zaɓuka na jam’iyyu da sauransu, shi ne zaɓe ta hanyar kaɗa ƙuri’a ko kuma masalaha ta hanyar yardar kowane ɓangare. To jam’iyyar APC ba ta biyo kowane layi cikin biyun ba a wannan gaɓa, kowane ɓangare zai nuna irin ƙarfi da ikon da ya ke da shi ne ya fitar da shugaba.

Gwamna da shugaban ƙasa da uwar jam’iyya su ne ke da haƙƙin samar da masalaha da daidaito a jam’iyyarsu idan irin haka ta faru. To tun kafin a akai ko’ina gwamna ya yi maganganu masu zafi akan Sanata Shekarau da ƴan tawagarsu, ya kira su da banza bakwai, ma’ana ba su ma da wani amfani, ko da su ko babu su ya na nufin za a yi komai, wanda hakan ne kuma ya fusata mabiyansu a Social Media su ma su ka hau rubuce-rubucen ramuwar gayya.

Dole a yanzu dama ɗaya ce ta rage wajen samar da masalaha a jam’iyyar kafin lokaci ya ƙure mata, damar ita ce ta shugaban ƙasa da uwar jam’iyya su yi abin da ya kamata a kan lokaci, a zauna a yi masalaha ta hanyar yi wa kowane ɓangare adalci. In ba wannan ba kuwa to jam’iyyar APC za ta cigaba da samun fitintinun da za su haifar mata hasara 2023.

A ƙarshen wasan zai kasance jam’iyyar ta faɗa cikin babban rikicin da babu mai warware shi sai kotu, kuma dole kotun za a shiga a cigaba da fafatawa har lokaci ya ƙure. Irin wannan matsaloli jam’iyyar CPC mai alƙalami ta shugaban ƙasa Buhari ta fuskanta a shekarar 2011, wanda hakan ne ya haifar mata rashin nasara a Jihohin ƙasar nan da dama tayadda da ba dan wannan fitintinu ba, to da kuwa ko ba ta samu shugaban ƙasa ba, to za ta iya samun Jihohi da dama, amma waɗannan rigingimu na cikin gida su ne su ka ɓarar mata da garinta.

Ko ma dai yaya za ta kaya a cikin jam’iyyar APC yau a Jihar Kano, namu ido, mu na ji, mu na gani, mu na kuma saurare, Allah Ya mana mai kyau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here