Rotimi Akeredolu na jam’iyyar APC ya lashe zaɓen gwamnan jihar Ondo

0
410

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar da Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da ya gudana ranar Asabar.

Babban Bature zabe na INEC, Farfesa Abel Idowu Olayinka, wanda shi ne Shugaban Jami’ar Ibadan ne ya sanar da sakamakon zaben a ranar Lahadi.

Akeredolu na jam’iyyar APC ya samu gagarumar nasara a wa’adi na biyu da yake nema inda ya lashe zabe a 15 daga cikin Kanan Hukumomin jihar guda 18.

Ya kayar da babban abokin hamayarsa, Eyitayo Jegede na jami’ar PDP a matsayi na biyu.

Mataimakin Gwamnan, Agboola Ajayi wanda ya yi takara a karkashin jam’iyyar ZLP shi ne ya zo na uku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here