Rundunar Sojan Nijeriya Ta Kashe ‘Yan Bindiga 17 A Katsina

0
124

Akalla mutum sha bakwai rundunar samamen ‘Operation Sahel Sanity’ suka hallaka tare da kame da dama a fafatawar da rundunar da ta yi kwanan nan a jihar Katsina, kamar yadda hedikwatar tsaro suka bayyana.

Daraktan yada labaran rundunar na riko, Birgediya Janaral  Bernard Onyeuko shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.

Onyeuko ya ce rundunar ‘Combat Team 1,’ a ranar 18 ga watan Yuli tare da taimakon rundunar sama sun yi nasarar cafke wani hatsabibin dan bindiga a wani sansani da ake kira ‘Dangote Camp’ dake cikin dajin karamar hukumar Jibiya dake jihar Katsina.

Har wala yau Hedikwatar tsaron ta ce ta kwato bindigogi guda biyar kirar AK 47 da kwanson harsasai 47, da manyan bindigu guda uku, da kuma Magazine na AK 47 guda biyu, sai kuma wadansu harsasai na musamman guda 152 da Babura bakwai wanda ‘yan bindigar suka gudu suka barsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here