Rushe Ginin Diflomasiyya A Ghana: Nijeriya Ta Yi Fushi

0
277

Gwamnatin Tarayya ta yi tir da matakin rushe gine-ginen Difilomasiyyarta biyu da ke birnin Accra na kasar Ghana tare da neman karin bayani daga gwamnatin kasar game da musabbin hakan.

Ministan harkokin wajen Nijeriyar Geoffrey Onyeama ne ya bayyana hakan a shafinsa dake Twitter jim kadan bayan bayyanar batun rushe ginin Diflomasiyyar, ya ce wajibi ne Ghana ta dauki matakin kare lafiyar ‘yan Nijeriya da ke cikin kasar.

Onyeama tuni gwamnatocin kasashen biyu suka fara tattaunawa kan batun wanda bayanai ke cewa an yi amfani da motar rusau wajen niqe gine-ginen Diflomasiyyar Nijeriyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here