Ruwan sama yana kawo mana cikas a yaƙi da ƴan bindiga a jihar Katsina – Masari

0
1479

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya ce ruwan sama da ake yi kamar da bakin kwarya na daya daga cikin kalubalen da hukumomin tsaron da ke yaki da ‘yan bindiga a yankin arewa ke fuskanta.

Masari ya kuma bayyana fargabar cewa rashin zaman lafiyan da ake fama da shi a sassan kasar nan na iya barazana ga samar da abinci a kasar.
Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a lokacin zantawarsa da manema labarai a gidan gwamnati bayan taron da ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.

Masari ya ce jami’an tsaron suna fuskantar kalubale wajen zirga zirgar motocin yakin sojoji a lokacin damina saboda laushin kasar da ke dajin da yan bindigar suke fakewa.

Amma duk da hakan ya bayyana gamsuwarsa cewa za a magance kallubalen kuma za a samu nasara a kansu.

Gwamnan ya ce, “Akwai daji masu girma da hanyoyi masu wahalar bi a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Tsakiya inda yan bindigan ke buya.

Yanzu lokacin damina mu ke, akwai wahalar tafiya da manyan motocin yaki na sojoji domin kasar laushi gare ta kuma ruwan sama ya yi yawa. Amma dai za a cimma buri. Babu abinda ba zai yi wu ba idan har akwai niyya kuma an dage.

Masari ya ce a halin yanzu akwai sojoji kimanin 2,000 a Katsina inda za su yi taron su na shekara wadda hakan alama ce da ke nuna wa yan bindigan cewa sojojin sun shirya tsaf don yin maganinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here