Ruwan sama zai ƙara adadin masu cutar korona a Najeriya – Gwamnatin tarayya

0
745

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ‘yan Najeriya su rika kiyaye ka’idojin rage yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19 musamman a yanayin damuna da aka shiga.

Kiran ya fito ne daga sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha wanda kuma shi ne shugaban kwamitin gwamnatin tarayya da ke yaki da cutar.

Yace ‘yan Najeriya su gane cewa cutar akwaita kuma tana da hadari da saurain yaduwa. Yace dolene a kara kula da kiyayewa wajan kamuwa da cutar lura da yanda yanzu ya koma sabuwa a kasashen Amurka da China.

Ya ƙara da cewa musamman a lokacin damuna wanda ake samun ciwuka irin su mura masu kama da cutar Coronavirus/COVID-19 dole a kara kiya yewa.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here