Saboda Korona Muna Kashe Naira Miliyan 15 Duk Mako A Bauchi-Gwamna Bala

0
2980

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ce gwamnatinsa tana kashe sama da naira miliyan 15 a matsayin Alawus ga ma’aikatan lafiya da sauran wadanda suke gaba wajen yaki da cutar annobar Korona.

Gwamna Mohammed ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a garin Bauchi a yayin da yake kaddamar da dakin gwajin cutar Korona ta jihar mai suna ‘Molecular Reference Laboratory for COVID-19.’

Gwamnan ya ce; kudin alawus din da ake kashe wa, ana kashe su ne wajen bibiyar wadanda masu korona suka yi hulda da su, kula da masu cutar da kuma matakan da ake dauka wajen dakile cutar da bada kariya ga masu cutar.

Ya ce gwamnatinsa na bai wa wadanda Korona ta kama kulawa, musamman wajen lura da irin abincin da suke ci, inda ake ba su abinci sau uku a kowacce rana. Ya ce wannan ne ma dalilin da ya sanya masu warkewa a jihar daga cutar suka fi a ko’ina a fadin kasarnan.

Gwamnan ya ce hatta gina dakin gwajin cutar ya samu ne sakamakon damuwar da gwamnatinsa ta nuna domin saukakawa masu fama da cutar, da kuma iyalan masu cutar da ma’aikatan lafiya, inda ya ce ma za a samar da dakin gwajin cutar zazzabin Lassa da shawara da sauran cututtuka ma a jihar.

Sai dai gwamnan ya tabbatar da cewa an gina asibitin ne tare da hadin guiwar Hukumar lura da ci gaban arewa maso gabas, NEDC da kuma NCDC, cibiyar dake dakile cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya.

Dakin gwajin na Korona, yana da karfin yiwa mutum 300 gwajin cutar a kowacce rana. Kamar yadda NCDC suka tabbatar.

Jihar Bauchi dai ya zuwa hada rahoton nan suna da masu cutar Korona guda 500, a inda 439 daga cikinsu suka warke, 12 suka mutu, 49 ake ci gaba da kula da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here