Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya cika shekara 59 da haihuwa: Abubuwan da ya kamata ku sani game da shi

0
219

 

An haifi Alhaji Aminu Bayero a kwaryar birnin Kano ranar 21 ga watan Agusta, 1961, gabanin mahaifinsa Ado Bayero ya zama sarkin Kano da shekara biyu.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya fara karatu a makarantar firamare ta Kofar Kudu daga 1967 inda ya kammala a 1974.

Daga nan ne kuma ya tafi zuwa kwalejin gwamnati ta Birnin ta Birnin Kudu a jihar Jigawa a yanzu, inda ya yi karatunsa na sakandare.

Alhaji Aminu Bayero ya halarci Jami’ar Bayero inda ya samu digiri a fannin aikin jarida da kimiyyar siyasa daga 1979 zuwa 1984.

Haka kuma ya yi aikin hidimar kasa a jihar Benue inda ya yi aiki a gidan talabijin na kasa NTA.S

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado ya fara aiki a kamfanin jiragen sama na Kabo Air, a matsayin jami’in hulda da jama’a daga 1985 zuwa 1990 inda ya riki matsayin darakta a kamafanin.

A bangaren kungiyoyi kuwa, Sarkin Kano Aminu Ado Bayero shi ne shugaban kungiyar masu wasan kwallon kwando ta jihar Kano, kuma shi ne uban kungiyar ‘yan asalin Ilorin.

Aminu Ado Bayero A Fagen Sarauta

A shekarar 1990 mahaifinsa Alhaji Ado Bayero ya fara ba shi mukamin sarauta, inda aka nada shi Dan Majen Kano kuma Hakimin Nassarawa.

Daga nan ne kuma aka kara masa girma zuwa Dan Majen Kano Hakimin Gwale a dai shekarar ta 1990.

A shekrar 1991 kuma likkafa ta kara gaba inda aka nada shi Turakin Kano kuma Hakimin Dala a watan Janairun 1991 zuwa Janairun 2001, ma’ana dai ya shekara 10 a wannan mukami.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya zama Sarkin Dawakin Tsakar Gida, Hakimin Dala daga watan Janairun 2001 mukamin da ya rike har zuwa 2014.

A watan Oktobar 2014 Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya nada shi a matsayin Wamban Kano kuma dan majalisar sarki. Ya rike mukamin har zuwa watan Mayun 2019.

A watan Disambar 2019 ne kuma Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nada shi Sarkin Bichi na farko bayan kirkirar sabbin masarautu.

A ranar 9 ga watan Maris din shekarar 2020 Aminu Ado Bayero wanda da ne ga marigayi Sarki Ado ya zama sarki na 15 a jerin Sarakunan Fulani a Daular Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here