Saura kaɗan ƴan Najeriya su fara shan jar miya – Buhari

1
617

Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya ce ƴan Najeriya za su samu sassauci kan halin matsin tattalin arziƙi da ake ciki da zarar cutar Covid-19 ta wuce.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a zantawarsa da gidan rediyon Freedom da ke Kano.

Garba Shehu ya ce, sanadiyyar cutar Corona babu ƙasar da tattalin arziƙinta bai durƙushe ba sai ƙasar China, a don haka halin matsin ba iya Najeriya ya shafa ba.

Duk da haka gwamnatin tarayya na iya ƙoƙarin ta wajen ɗaukar matakan kawo sassauci ga al’umma, kuma muna fatan ba zai ɗore ba sauƙi na nan zuwa cikin yardar Allah a cewarsa.

 

Freedom Ra dio Nigeria

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here