Jama’a da dama musamman a kafofin sada zumunta na ci gaba da nuna alhini bayan cika shekara 21 da rasuwar shahararren mawakin Hausa Dokta Mamman Shata Katsina.
Shata ya rasu ne a ranar 18 ga watan Junin shekarar 1999 a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano.
Jama’a da dama a shafukan sada zumuntar na tunawa da shi da wakokinsa da gudunmuwar da ya bayar wajen ci gaban harshen Hausa da nishadantar da jama’a.
Wane ne Mamman Shata Katsina?
An haife Shata a garin Musawa a jihar Katsina a shekarar 1923
Ya yi tallan goro da alewa lokacin da yake saurayi
Ya shafe fiye da shekara 50 yana salon wakar baka
An rubuta dimbin takardun da kasidu game da rayuwarsa
Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ta ba shi digirin girmamawa
Gwamnatin Najeriya ta ba shi lambar girmamawa ta MON
Ya yi wakoki a fannoni daban-daban na rayuwa
Ya yi dimbin wakoki wadanda ya ce shi kansa bai san adadinsu ba
Ya ziyarci kasashe da dama ciki har da Amurka da Birtaniya da Saudiyya
Ya bar ‘ya’ya 19 da kuma jikoki da dama
An binne shi ne a ƙaramar hukumar Daura ta jihar Katsina.