Shaye-shaye: Yadda wani Uba ya ɗaure Ɗansa tsawon shekaru 7 a Kano

0
1994

Maƙwabta da haɗin gwiwar ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Human Right Network da kuma jami’an ‘yan sanda, sun samu nasarar kuɓutar da wani matashi da ake zargin mahaifinsa ya ɗaure shi a gida har tsawon shekaru 7 a unguwar Farawa dake Kano.

Matashin mai suna Ahmad Aliyu mai shekaru 32 a duniya mazaunin Unguwar Farawa Babban layi a yankin ƙaramar hukumar ƙumbotso yana tsare ne har shekaru 7 ba tare da samun kulawar da ta dace ba, ta ci da sha da sutura kamar yadda wanda suka ceto shi suka bayyanawa jami’an tsaro.

Ɗaya daga cikin mutanen, ya nemi a sakaya sunansa ya ce, mahaifin matashin ne ya killace shi a gida, tare da haɗin kan matarsa kasancewar mahaifiyarsa ta rasu, bisa yadda mahaifin nasa ya ce, ya fara shaye-shaye.

Haka kuma ya shaida wa manema labarai cewa, ko da ‘yan ƙungiyar ta Human Right Network da DCO na ofishin ‘yan sanda na Farawa suka je gidan domin kuɓutar da matashin, matar mahaifin nasa ta ƙeƙasa ƙasa cewa baya gidan amma da suka kutsa kai ciki suka gano shi.

Amma daga baya jami’an ‘yan sanda sun hana zuwa ganinsa sakamakon yanayin da yake ciki, kuma daga bisani an garzaya da shi asibiti domin bashi agajin gaggawa.

Abubakar Muhammad Usman

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here