Shekara ɗaya da rufe iyakokin Najeriya: Ko matakin ya amfani talaka?

0
1172

Al’ummomin da ke zaune a garuruwan da ke kan iyakokin Najeriya sun bayyana cewa kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba shekara guda bayan gwamnatin ƙasar ta rufe iyakokinta da ke kan tudu.

A watan Agustan 2019 ne gwamnatin kasar ta rufe iyakokin nata da zummar daƙile yawaitar fasa-kwauri da kuma bunƙasa tattalin arziki, ko da yake ‘yan kasar da dama sun koka kan matakin.

Hukumar hana fasa-ƙwauri, wadda ta yi ruwa ta yi tsaki wajen ganin an yi aiki da rufe iyakokin, ta bugi ƙirji game da irin nasarorin da ƙasar ta samu saboda matakin da ta dauka na rufe iyakokin tudu ta fuskoki daban-daban na rayuwa.

Joseph Attah, kakakin hukumar kwastam na ƙasa, ya shaida wa BBC cewa da Najeriya ba ta ɗauki matakin rufe iyakokin nata wanda ya taimaka wajen inganta noma ba, to da ta fuskanci matsala ta ɓangaren abinci bayan ɓullar annobar korona, da ta tilasta wa ƙasashen duniya rufe ƙofofinsu.

“Harkar noma ta samu inganci, shi ya sa (matakin) ya rage wahalar da ake sha sakamakon zuwa koronabairus.

Na biyu shi ne ta hanyar tsaro; duk da dai ba a shawo kan (matsalolin) tsaro kwata-kwata ba a Najeriya, amma duk mai hankali ya san cewa abin (yanzu) ba kamar yadda yake da ba,” in ji shi.

Sai dai al`ummomi mazauna iyakokin Najeriya, na ganin cewa maimakon Najeriya ta ƙaru da matakin nata, raguwa ta yi. Saboda haka a nasu ra`ayin, garin gyaran gira ne Najeriya ta je, ta rasa ido.

Shin ‘yan Najeriya sun ga amfanin rufe kan iyakokin kasar?

Sada Soli Jibia ɗan majalisar wakilai da ke wakiltar wasu daga cikin al`umomin Najeriya mazauna kan iyaka, ya ce rufe iyakokin bai yi amfani ba

‘Kowa ya san halin da ake ciki’

 

A cewarsa: “Idan an ce an rufe ne saboda kada a shigo da makamai, amma kowa ya san halin da ake ciki a waɗannan yankuna.

Idan kuma an ce an yi don maganar fetur, to ko kwanan nan mun ji an ce an fitar da wasu tankoki wajen ɗari da ashirin da wani abu har wani jami’in kwastam ya rasa aikinsa.”

Ya yi kira ga mahukunta su sauya fasali kan rufe iyakokin yana mai cewa ba ƙaramar asara hakan ya janyo ba.

Wani mazaunin kan iyakar Najeriya a jihar Sokoto ya shaida wa BBC cewa rufe iyakokin ya kawo hauhawar farashin kayayyaki a yankinsu.

Sai dai kakakin hukumar kwastan Mr Joseph Attah ya ce jami`ansu da na sauran hukumomin da ke aikin haɗin gwiwa suna bakin ƙoƙarinsu wajen yaƙi da masu fasa-kwauri.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here