Shin Ko Ƙiba Ta Na Shafar Yanayin Lafiyar Maza Ta Fuskar Jima’i ???

0
8862

Shin Ko Ƙiba Ta Na Shafar Yanayin Lafiyar Maza Ta Fuskar Jima’i ???

DAGA Dokin Ƙarfe TV.

A duk lokacin da ake maganar ƙiba, abu na farko da ake nazarin ya haifar da ita shi ne rashin motsa jiki ko ƙarancin motsa jikin. Ƙiba matsala ce da ke haifarwa ɗan adam ƙarin wasu matsalolin ko cututtuka ko kuma jinyoyi kala daban-daban waɗanda su ka haɗa da: hawan jini, rashin kuzari, ciwon suga, ƙarancin samun bacci da kuma gajiya a ya yin jima’i.

Mafi yawan mutane masu ƙiba su na fama da matsalolin ƙarancin sha’awar jima’i, masana sun tabbatar da cewa kaso hamsin da uku na maza ƴan shekaru 40 zuwa 70 su na fama da ƙarancin sha’awar jima’i. Akwai abubuwa da dama da ke haddasa matsalar daga ciki akwai:

1. Yawan Shekaru.
2. Matsanancin bugawar jini.
3. Ƙiba. Da sauransu.

Ƙiba idan ta yi yawa ta na haifar da duk waɗannan matsaloli haɗi da ciwon suga da hawan jini, tare kuma da haifar da ƙarancin sha’awar jima’i ko gajiya nan da nan idan an fara. Idan yawan shekaru su ka haɗu da yawan ƙiba, to haɗarin ƙarancin sha’awar kuma ya fi girma. Ƙarancin sha’awa kuwa matsala ce da ke haifar da damuwa mai tsanani ga al’umma.

“Idan ka kamu da lalurar ƙiba, ka na cikin hatsarin kamuwa da ciwon suga sosai a lokuta biyu zuwa uku saɓanin wanda ba shi da kiba hatsarin da ya ke ciki na kamuwa da ciwon sugan bai kai naka ba, fiye da kaso 50 na maza masu ciwon suga su na fama da matsalar ƙarancin sha’awa”. Cewar Elizabeth Selvin, Phd, MPH, ƙwararriyar masaniyar lafiya.

Binciken masana ya tabbatar da cewa mafita ga mutane masu ƙiba shi ne su riƙa kiyayewa da cin duk wasu nau’ikan abinci mai ƙara ƙiba. Su kuma kula da lafiyarsu ta hanyar motsa jiki akai-akai tare da tuntuɓar masana kiwon lafiya domin neman shawarwari. Gwargwadon yadda mutum ya ke rage ƙibarsa, gwargwadon yadda kuzarinsa da sha’awarsa ta jima’i za ta na ƙaruwa da kuma jimawa daidai gwargwado.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here