Shin Ko Ƴan Nageriya Za Su Amince A Ƙarawa Shugaba Buhari Shekaru 4 ???

0
30554

Duba da yadda wa’adin zangon mulki na biyu na shugaban Nageriya Muhammadu Buhari ya ke kusa da ƙarewa a 2023, hakan ya sanya wasu al’ummar ƙasar sun fara kiraye-kirayen ya kamata a ƙara masa wasu ƙarin shekaru huɗun domin ya samu nasarar kammala ayyukan da ya faro, sannan kuma ga halin da ƙasar ta ke ciki na matsalar tsaro wacce za ta iya sanyawa a kasa samun damar gudanar da zaɓe a 2023.

Shin a matsayinka/ki na ɗan/ƴar Nageriya, ko kun amince a yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima domin a ƙarawa shugaban ƙasa Buhari lokaci saboda ya samu damar ƙarasa ayyukan da ya faro kamar yadda ake faɗa ???

Shin waɗanne ayyuka ka sani wanda shugaba Buhari ya faro waɗanda in an ƙara masa lokaci ka ke da tabbacin zai kammala su talaka ya amfana ? Ya kuma ka/ki ke kallon salon kamun ludayinsa a cikin shekaru shida da ya yi yanzu, shin ko kwalliya na biyan kuɗin sabulu ? Shin a misali inda za a ce ƙuri’arka/ki kaɗai shugaba Buhari ya ke nema domin samun ƙarin wa’adin shekaru 4 za ka/ki amince masa ??????????

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here