Shugaba Buhari ba ya ɗaukar shawara – Mongono

0
596

A yayin da shugaban Muhammadu Buhari ya bai wa hafsoshin tsaron kasar nan wa’adin sabonta dabarun yaki da ‘yan ta’adda, masana lamurran tsaro sun bayyana cewa, shugaba Buhari ba ya daukar shawarar da ake ba shi kan tsaro.

A yayin zantawa da sashen hausa na RFI, Hussaini Mongono, masanin lamurran tsaro a Najeriya ya ce, babu wasu sabbin dabarun da za a yi amfani da su wajen kawo karshen matsalar tsaron da ke addabar kasar, illa kawai ya sallami hafsoshin tsaron kasar.

“Shugaba Buhari, shugaba ne da bai jin shawara, bai so a fada masa abin da ya kamata ya yi, shi dan adam ne kuma babu yadda za a ce ya iya komai” inji Mongono.

A baya bayan ‘yan Najeriya da dama ciki har da ‘yan majalisun kasa sun jaddada kira ga shugaba Buhari da ya sauke shugabannin rundunonin tsaron kasar bisa gazawarsu wajen kare rayukan al’umma musamman a jihohin Borno da Zamfara da Katsina da Sokoto da Kuduna da ke fama da tashe-tashen hankula, abin da ke sanadin mutuwar dimbin talakawa akai akai.

A ganawar da ya yi da hafsoshin tsaron a cikin wannan makon, shugaba Buhari ya gargade su cewar, muddin suka gaza shawo kan matsalar, to zai dauki tsattsauran mataki.

Ko a baya bayan sai da gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya fito fili yana cewa, ana yi wa gwamnati zagon kasa a kokarinta na yaki da matsalar tsaro a kasar.

Gwamnan ya tsallake rijiya da baya a wani harin kwanton bauna da aka kaddamar kan ayarinsa a kan hanyarsa ta zuwa Baga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here