Shugaba Buhari ya aikewa da Sarkin Makka wasiƙar dubiya

0
3458

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na ya aikewa Sarkin Saudiyya Salman Bin Abdulaziz da wasika bayan da aka kwantar da basaraken a asibiti.

“A madadina, da gwamnatina da kuma mutanen Najeriya, ina yi wa sarkin Saudiyya fatan warkewa cikin gaggawa. Sarki Salman ya kasance daya daga cikin shugabannin duniya mafiya inganci da na taba haduwa da su” in ji shugaba Buhari.

Buhari ya jaddada cewa “Sarki Salman babban aboki ne ga Najeriya kuma bai taba kin taimaka wa kasar ba a yayin lokacin bukata, saboda haka ina fatan ya samu sauki cikin gaggawa.”

Shugaban ya fadi hakan ne a cikin wata sanarwar da ya fitar mai dauke da sa hannun kakakin fadarsa Malam Garba Shehu.

A safiyar yau ne kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA ya bayanna cewa an kwantar da sarkin a wani asibiti da ke Birnin Riyadh sanadiyyar fama da yake yi da matsalar mafitsara.

Haka ita ma Jaridar Wall Street Journal ta bayyana cewa an kwantar da basaraken ne bisa matsalar mafitsara da yake fama da ita.

Tun shekarar 2015 sarkin mai shekaru 84 ya ke mulkin kasar ta Sa udiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here