Shugabar Ƙungiyar #WeBelieve Maryam Shetty Ta Samu Digirin Girmamawa Zuwa Matsayin Dakta 

0
30445

Maryma Shettima, shugabar ƙungiyar #WeBelieve, ƙungiyar magoya bayan jam’iyyar APC ta ƙasa da kuma yaɗa ayyukan gwamnatin shugaban ƙasa Buhari, ta samu digirin girmama zuwa matsayin Dakta a saboda irin ɗumbin gudunmawar da ta ke ba wa al’umma.

A cikin wasiƙar sanar da lambar yabon mai ɗauke da kwanan wata 27 ga watan Octoba, 2021, jami’ar Ecole Superieure de Gestion et de Technologie (ESGT University), da ke birnin Benin ta bayyana cewa lambar yabon girmamawa ce wacce ake ba wa nagartattun mutane waɗanda su ka taka muhimmiyar rawa ga cigaban rayuwar al’umma a fannin: Ilimi, siyasa, tattalin arziƙi wajen tallafawa mutane da jarin dogaro da kai, da kula da harkokin zamantakewa da nazariyyar halayyar ɗan adam, da harkar cigaba.

“Shugabanci nagari da hangen nesanki sun bayyana dukkan nagartarki”. Wasiƙar ta faɗa akan Hajiya Shettima.

Wacce aka fi sani da Maryam Shetty, ƴar gwagwarmayar siyasa ce da harkokin al’umma kuma ƙwararriya a fannin ilimin kula da lafiyar waɗanda su ka gamu da wata lalura.

An haife ta a gidan sarautar Kano, Hajiya Shettima, ta fara karatunta matakin farko a Kano daga bisani ta tafi makarantar gwamnatin tarayya ta duba lafiyar waɗanda su ka raunata a jami’ar Bayero Kano inda ta kammala da babban sakamako.

Ta yi aiki da Asibitin Ƙashi na Dala da Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano a Jihar Kano kafin daga bisani ta tafi ƙarin karatu birnin Landan. Ta samu shaidar kammala karatun digiri na biyu a jami’ar East da ke Landan inda ta naƙalci kula da jikkata da lafiyar ƴan wasa.

Ta na cikin tawagar ƙwararrun masana kiwon lafiya na wasan Olamfic na birnin Landan inda ta yi aiki da manyan ƙwararru ciki har da Jamaica’s Usain Bolt wanda ya lashe kambun yabo na duniya.

Har wa yau Maryam ta samu shaida da zama mai gabatarwa ta tawagar Ƙingian da yaƙi da tarzoma, bisa nazariyyar Dakta Martin Luther King Jr. daga jami’ar Emory a ƙasar Amurka. Sannan kuma ta samu shaidar lashe gasar ƙalubale ta al’umma ta ƙarni na 21 daga Jami’ar Virginia.

Ta na da gogewar ayyuka a duka fannonin na lafiya da ƙuma ƙungiyoyin samar da cigaba na duniya inda ta yi aiki a ƙarƙashin shirin Ukaid, da asibitin fadar shugaban ƙasar Nageriya da tawagar kula da yara. Shettima ta kasance mai ƙaunar al’umma da samar da tsare-tsaren cigabansu, musamman a fannin ilimi inda ta jagoranci sabunta makarantu a Jiharta ta asali Kano a ƙarƙashin #GivingBack initiative.

A saboda ɗumbin ƙoƙarinta da kishinta, ta taɓa wakiltar Nageriya a zauren taro na majalissar ɗinkin duniya a ƙarƙashin kwamitin daidaito da adalci da yaƙi da rashawa da cin hanci.

A siyasance ta taɓa kasancewa memba a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa kan ayyuka na musamman.

Sannan kuma ta taɓa zama memba a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na mata da matasa da tsare-tsaren harkokin sadarwa.

Har wa yau ta kasance ɗaya daga cikin membobi bakwai na kwamitin jam’iyyar APC da jam’iyya ta tura halartar taron zaɓen shugabannin jam’iyyar a Jihar Delta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here