Siyasa: Lokaci ya yi da za a sauya fasali da tsarin Najeriya – Nasir El-Rufai

0
124

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya ce lokaci ya yi da ya kamata a sauya fasalin Najeriya domin bai wa jihohi ƙarin iko kan albarkatun ƙasa da ‘yan sanda.

Da yake magana a taron cika 50 da kafa Gidan Arewa a Kaduna ranar Asabar, El-Rufai ya ce sauya tsarin mulkin ƙasar na cikin abin da zai “kawo cigaban Najeriya”.

Gwamnan wanda ya bayar da misali da wani rahoton kwamitinsu na jam’iyyar APC a 2018 game da sauya fasalin Najeriya, ya ce akwai buƙatar a ƙara wa jihohi ƙarfin iko kan albarkatun ƙasa da sauran abubuwa.

Aikin kwamitin wanda APC mai mulkin Najeriya ta kafa a 2017 ƙarƙashin jagorancin El-Rufai shi ne, tsara yadda jam’iyyar ke kallon sauya fasalin ƙasa da zummar kowane ɗan Najeriya ya amfana daga cikakken tsarin jamhuriya, wanda Najeriya ke kai.

Daga cikin shwarwarin kwamitin, El-Rufai ya nuna cewa jihohi za su samu ƙarin iko kan albarkatun man fetur da gas da ma’adanai da gidajen yari da kuɗin haraji da yi wa kamfanoni rajista da sauransu.

Ya ce: “Ni ban san wata mazaɓa ba da ke adawa da manufar ƙara wa jihohi ƙarfin iko kan ma’adanai domin kyautata rayuwar waɗanda suke mulka.

“Hakan zai bai wa gwamnatocin jiha damar daina miƙa wa Gwamnatin Tarayya da shugaban ƙasa dukiya alhalin akasarin matsalolin da ‘yan ƙasa ke fuskanta za a iya magance su a matakin gwamn atin jiha.”

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here