Siyasar Kai Da Halinka 2023: Shawara Zuwa Ga Matasan Arewa – Bashir Abdullahi El-bash

0
212

-Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Zai Kammala Wa’adinsa Na Shekaru 8 A Shekarar 2023, Shi Da Shugabancin Nageriya Kuma Har Abada Kamar Yadda Kundin Tsarin Mulki Ya Tanadar, Lokaci Ya Yi Da Ya Kamata Matasan Arewa Su Yi Karatun Ta Nutsu Su Yi Abin Da Zai Fisshe Su A Siyasar Shekarar 2023.

Kamar yadda mu ka sani shugaban ƙasar Nageriya Mallam Muhammadu Buhari shi ne ɗan siyasa ɗaya tilo mafi farin jini a Nageriya musamman ma yankin Arewa. Akwai ɗumbin al’umma waɗanda babu ruwansu da siyasa sai a sanadiyyar shugaban ƙasa Buhari. Sannan akwai ɗumbin ƴan siyasa waɗanda su ke ɓuya a bayan shugaban ƙasa Buhari su ci zaɓe saboda duk wanda ya ke jam’iyyar Buhari ya na cin albarkacin Buhari.

Wannan dalili shi ne ya sanya ƴan siyasa da dama a Arewacin Nageriya ba sa temakon jama’a saboda ba su san muhimmancin jama’ar ba, ba su san wahalar tara jama’a ba, ba su san wahalar riƙe jama’a ba, jama’ar su ka gani kawai a tare sun bi su albarkacin me albarka.

To Hausawa su ka ce wai komai ya yi farko zai yi ƙarshe, yanzu dai shugaban ƙasa Buhari lokacinsa ya ƙare a siyasa, ya gama cin zamaninsa, kuma babu tabbacin zai ɗaga hannun kowa a siyasar 2023, sannan ko ya ɗaga hannun wani ma bai zama lallai jama’a su bi ba kamar yadda su ka bi a baya 100% saboda su na ganin an ɓata musu kan wasu abubuwan.

Saboda haka 2023 ya kamata ace ta zama dama ga matasan Arewa su tsaya su yi karatun ta nutsu su bi mutanen da za su taimaka musu. Matasan Kudu sun daɗe da yin nisa a wannan karatun, mafi yawansu babu ruwansu da wata jam’iyyar siyasa duk wanda zai taimake su shi su ke yi, kuma ya na fitar da su kunya. Ana temaka musu lokacin da ake fafutukar samun mulkin, sannan ana yin nasara su ke kai (CV) ɗinsu a sama musu aiki.

Saboda haka ina ba wa matasan Arewa shawara su tsaya su tara hankalinsu wuri guda a wannan siyasa ta 2023 domin tun daga yanzu har an fara kaɗa ta, su bi duk wanda zai temaka musu. Kafin su bi mutum a siyasa ko su tallata shi a kafafen sadarwa na zamani su fara duba na kusa da shi ko mutanen da su ke jikinsa ko yaransa shin ya temaka musu ? Idan har ya temaka musu to akwai yiyuwar su ma ya taimaka mu su, amma idan bai temakawa waɗanda su ke tare da shi ba akwai yiyuwar su ma ya watsar da su bayan an ya yi nasara.

Tabbas 2023 shekarar siyasa ce mai taken kai da halinka, wanda duk ya temaki jama’a a lokacin da ya ke da dama ko ta siyasa ko ba ta siyasa ba, ba shakka shi jama’a za su yi a wannan siyasa, domin duk ruguntsumin rayuwar da ake yi a duniya amfanin a iya duniyar ne kawai, in mutum bai temaka maka a duniya ba, babu wani temako da zai iya yi maka bayan mutuwa. Yadda mutane su ka gwaru, ba na raba ɗaya biyu a 2023 za su bi waɗanda su ka taimaka musu ne ko su ke da tabbacin za su temaka musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here