Sojin Nijeriya Sun Hallaka Kwamandojin Boko Haram A Borno

0
102

Rahotanni daga jihar Borno sun nuna cewa rundunar sojin Nijeriya sun hallaka Kwamandojin Boko Haram. Rundunar Sojin ne ta tabbatar da hakan, inda ta ce dakarunta sun yi nasarar halaka wasu kwamandojin mayakan Boko Haram a yayin wani artabu da suka yi a jihar Borno.

Hedikwatar tsaron Nijeriya ta ce, dakarun sojin na ta sun kaiwa mayakan samame ne a kan iyakar Nijeriya da Kamaru, lokacin da suke kokarin tsallakawa zuwa cikin dajin Sambisa. A cikin sanarwar, sun tabbatar da cewa sojin Nijeriyar sun kuma yi nasarar kwace makamai, tarin alburusai, Mota da kuma kekuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here