Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Boko Haram 17 A Jihar Borno

0
4089

Rahotanni sun bayyana cewa harin mayakan Boko Haram ya hallaka Sojin Nijeriya 37 akan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damboa da ke jihar Borno mai fama da hare-haren ta’addanci.

Harin wanda ya faru ne tun a Talatar da ta gabata, a jiya Laraba ne rundunar Sojin Nijeriyar ta tabbatar da faruwarsa ga manema labarai sai dai ta bayyana cewa Soji biyu kadai ne suka rasa rayukansu.

Cikin sanarwar da Daraktan yada labaran ma’aikatar tsaron Nijeriya, Manjo Janar John Enenche ya fitar, ya bayyana cewa suma bangaren dakarun Sojin sun kashe mayakan na Boko Haram 17 a farmakin wanda aka fafata tsakanin bangarorin biyu.

Haka zalika sanarwar ta ce galibin mayakan na Boko Haram da suka  tsira a fafatawar, sun gudu ne da mummunar raunin harbi a jikkunansu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here