Sojojin Najeriya na da makamai fiye da ƴan ta’addar Boko Haram – Buhari

0
5351

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jaddada muhimmancin kare fararen hula da kuma kawo karshen tashe tashen hankulan da suka addabi kasar nan.

Buhari ya bukaci inganta dangantaka tsakanin jami’an tsaro da al’ummomin da suke aiki a cikin su, musamman wajen musayar bayanan asiri, yayin da ya bukaci kwamandojin tsaro da jagorancin yaki da batagari da su tabbatar da kare lafiyar fararen hula.

Haka kuma shugaba Buhari ya amince da rawar da talauci da rashin aikin yi ke takawa wajen ruruta matsalar tsaro a fadin ƙasar nan, inda ya bukaci hadin kai a matakai daban daban domin shawo kan matsalar.

Buhari yayi watsi da ikrarin cewar ƴan ta’addar da ke Yankin Arewa Maso gabashin kasar nan sun fi dakarun Najeriya makamai da kudade, inda yake cewa yanzu haka ƴan ta’addar farautar abinci suke yi wajen kai hari kasuwanni da gidajen jama’a domin samun abinda za su ci.

Shugaban kasar ya sake kalubalantar hafsoshin tsaron kasar nan wajen musayar bayanai da kuma aiki tare domin ganin an kawo karshen wadannan matsaloli da suka addabi Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here