Sojojin Nijeriya sun kashe shugaban ƴan bindiga tare da ceto mutane 32

0
4445

KoRundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da kashe wani shugaban kungiyar ‘yan bindiga tare da ceto mutane 32 da aka sace, yayin wani samame a yankin tsakiyar kasar nan.

Kakakin rundunar sojin John Enenche ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa cewa, an kaddamar da samamen ne a maboyar ‘yan bindigar dake kauyen Tomayin na jihar Benue dake arewa maso tsakiyar kasar.

John Enenche ya ce an kashe Zwa Ikyegh, shugaban wata kungiyar ‘yan bindiga a jihar Benue ne lokacin da sojojin ke farautar ‘yan bindigar, inda wasu daga cikinsu suka tsere da raunukan harbi.

Ya kara da cewa, samamen ya kai ga ceto mutane 32 da ‘yan bindigar suka sace, wadanda tuni aka hada su da iyalansu, ciki har da wadanda ake rike da su sama da wat a guda

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here