TETFund Za Ta Samar Wa Da Daliban Jami’a Dakunan Kwana 200,000 A Fadin Kasarnan

0
178

Daga Muhammad A. Dalhatu

Hukumar dake bai wa makarantun gaba da Sakandare Tallafi ta Nijeriya, TETFund ta bayyana cewa ta damu matuka da rashin wadatattun dakuna a makarantun gaba da Sakandare dake fadin kasarnan, inda ta yi alkawarin cewa ta dau aniyar samar da dakunan kwana guda dubu dari biyu a makarantun gaba da Sakandare dake fadin kasarnan domin magance wannan matsalar na rashin wuraren kwanan dalibai.

Kashim Ibrahim-Imam, shugaban amintattun hukumar, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai ciki harda wakilin Jaridar Madubi jim kadan da kammala taron membobin hukumar na 2020 kan jaddada kudurorinsu wanda suka yiwa take da “ Consolidating TETFund as a Model Intervention Agency for Nigeria’s Knowledge Economy.”

Taron ya gudana ne a ranar Laraba a birnin tarayya Abuja. Ibrahim-Imam ya bayyana damuwarsa bisa yadda matsalar rashin dakunan kwana da rashin ingantaccen intanet ke addabar makarantun gaba da Sakandare a Nijeriya duk da irin gudummawar da TETFund take bayarwa.

Ibrahim-Imam ya ce kwamitin amintattu na hukumar; “Sun damu matuka da abubuwa biyun nan, matsalar rashin wadatattun dakunan kwanan dalibai da kuma bangaren ICT, duk da tallafin da TETFund take bayarwa. Amma har yanzu makarantunmu na fama da matsalar azuzuwan karatu, bincike, dakunan nazari, dakunan kwana da bangaren ICT.” Inji shi.

Ya nuna yadda a bangaren dakunan kwana, ya zama kashi 10 zuwa 15 ne kawai na dalibai ke iya samun dakunan kwana. Inda ya bada misali da Jami’ar Abuja, inda ya ce wurin dakunan kwanan dalibai da bai wuce dubu ba kawai suke da shi cikin dalibai sama da dubu Talatin. A yayin da Jami’ar Kalaba ita ma wurin dalibai dubu biyu kawai take da shi cikin dalibai fiye da dubu hamsin.  Inda ya ce; “Wannan ya nuna kaso 3.3 ne da 3.7 kawai na daliban ke iya dauka.” Ya tabbatar.

Kwamitin amintattun ya bada shawarar hada hannu da kamfanunnuka masu zaman kansu bisa yarjejeniya wajen samar da dakunan kwanan, tare da bayyana cewa za su yi duk mai yiwuwa ma wajen samar hanyoyin karatu ta Intanet, “idan ma ya yiwu harda jarabawa ta hanyar Intanet.” Inji shi.

 

Da yake na shi bayanin, shugaban TETFund din, Farfesa Suleiman Elias Bogoro, ya bayyana cewa fadar shugaban kasa ta amince da kaddamar da bincike kan abin da ya shafi lafiya a Kwalejin horas da ma’aikatan lafiya shida dake yankuna shida na kasarnan, wanda ya ce wannan zai bai wa TETFund damar samar da cibiyoyi 12 na gwajin cutar Korona da kuma cututtuka masu yaduwa, inda za su samar da biyu a kowanne yanki na Nijeriya.

Farfesa Bogoro har wala yau ya ce; shugaban kasa ya amince da fitar da Naira biliyan 7.5 na kaddamar da bincike a shekarar 2020, wanda wannan ya sanya TETFund ta zama wacce ta fi kowacce hukuma samun kudin bincike a kasarnan.

Har wala yau ya bayyana cewa; kwamitin amintattun sun amince a fitar da naira miliyan 200 domin daukar nauyin bukatar da jami’o’i da NAFDAC suka turowa hukumar domin binciken maganin cutar Korona.

-Jaridar Madubi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here