Trump Ya Sake Jaddada Cewa Zai Iya Fadi Zabe

0
144

Da alama shugaban Amurka Donald Trump gabansa ya fara faduwa, inda ya fara sanyaya duba da yadda ya bayyana cewa ba zai samu nasarar ba a zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba.

Wannan zancen na sa shi ne karo na biyu da ya yi a wannan makon, inda yake cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden zai kada shi a zabe mai zuwa.

A wata hira da ya yi da Sean Hannity ta tashar Fox News, shugaba Donald Trump ya nuna alamun bada kai bori ya hau, inda yake cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden zai kada shi a zaben watan Nuwamba mai zuwa.

A hirar Trump ya ce Biden zai samu nasarar ce saboda wasu mutane basa son sa a Amurka, kuma wannan shi zai baiwa tsohon mataimakin shugaban nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here