Tsohon Kwamishina A Gombe Farfesa Wade Ya Rasu

0
156

Allah ya yiwa tsohon Kwamishinan manyan makarantu na jihar Gombe, Farfesa Isa Mohammed Wade Rasuwa. Ya rasu ne da safiyar yau Asabar.

Majiyarmu ta labarto cewa an yi masa jana’iza ne da yammacin yau Asabar 27 ga watan Yunin 2020. Ya rasu ya bar mata da ‘ya’ya.

Kafin rasuwarsa, jigo ne a kungiyar Malaman jami’o’i, ASUU. Kuma ya rike mukamin Kwamishinan ilimin manyan makarantu a jihar Gombe a karkashin mulkin tsohon gwamnan jiharm, Dan Kwambo.

Sannan yana cikin na gaba-gaba da ya nuna sha’awar tsayawa takarar zama gwamna a cikin jam’iyyar PDP domin ya gaji maigidansa.

Ya rike mukamai daban-daban kuma a kungiyar ASUU a matakin kasa da inda yake. Kafin zamansa Kwamishinan, yana koyarwa ne a Jami’ar gwamnatin tarayya dake Abuja. Inda ya bada gudummawa wajen farfado da ASUU a jami’ar.

Bayan kwashe shekara takwas a matsayin Kwamishina, Farfesa Isa ya koma jami’arsa, inda ya ci gaba da karantarwa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here