Tsohon Sanata Ya Jinjinawa Farfesa Adamu Bisa Gina Jami’a A Kano

0
3233

Sanata Bello Hayatu Gwarzo ya jinjinawa shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University, Nijer (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa samar da irin Jami’ar ta Nijer a jihar Kano.

A halin yanzu, Farfesa Adamu Gwarzo na gina Jami’ar MAAUN ta Nijeriya a yankin Hotoro dake cikin garin Kano. Sanatan ya jinjinawa Farfesa Gwarzo ne a yayin da ya kai ziyara a ginin Jami’ar dake Kano.

Sanata Gwarzo ya ce ginin Jami’ar da Farfesa Gwarzo yake ginawa A Kano, ya nuna jajircewarsa da kumajinsa wajen bunkasa kyakkyawar mu’amala da kuma tattalin arzikin jama’arsa.

“Tabbas wannan aikin ya nuna yana da kishin al’ummarsa wajen samar da wannan gagarumin aikin da ya shafi ilimi, tabbas abin jindadi ne da murna ne ganin yadda aikin nan ya shafi bangaren ilimi.” Inji shi.

Har wala yau ya nuna cewa Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo yana da al’ummarsa a zuciyarsa, inda yake bada gudummawarsa ta hanyar ilimi. Sannan ya bayyana Farfesa Gwarzo a matsayin mutum da ya maida hankali wajen ci gaban jiharsa da ma kasa baki daya.

“Akwai bukatar dukkanin al’umma su jinjinawa Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa wannan aikin da ya dauko duk da akwai mutanen da suka fi shi dukiya, amma kuma ba su da kishin da yake da shi,” ya jinjina.

Inda a karshe ya yi kira ga gwamnnatin tarayya da ta jihar Kano da su ba shi gudummawa da tallafi wajen ganin ya kammala aikin nan da ya dauko, tare da yin kira da a yi koyi da Farfesa Gwarzo a daidai lokacin da ake da bukatar jami’o’i a Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here