Tun ranar da Sarkin Zazzau ya rasu, ba na iya bacci sai na sha magani – El Rufai

0
155

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufai, ya bayyana cewa tun ranar Lahadi da aka sanar masa da rasuwar Sarkin Zazzau, bai sake bacci ba sai ya sha magani saboda baƙin ciki.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wurin taron addu’ar uku na Marigayi Mai martaba Sarkin Zazzau, Dakta Shehu Idris wanda ya rasu a ranar Lahadi.

Manyan mutane da dama sun halarci addu’ar uku da aka yi a yau irin su Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da Gwamnan Jigawa Abubakar Badaru, da Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi da na Filato Simon Lalong.

BBC  Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here