Wani ƙaton Ɓera ya tilasta wa jirgin Air India saukar gaggawa

0
3406

Kamfanin jiragen sama na Air India ya ce wani bera da aka gano a dakin matuka daya daga cikin jiragensa mai dauke da fasinjoji 200 ya tilasta wa jirgin sauka bayan ya kwashe sa’oi 3 a sama akan hanyarsa ta zuwa birnin London daga Mumbai.

Kamfanin ya ce ya dauki matakin ne domin kare lafiyar fasinjojinsa saboda yadda aka san cewar beran na iya cinye wata waya da za ta iya haifar da matsala a jirgin.

Kamfanin ya ce an sauya wa fasinjojin wani jirgin, kana ana aikin feshi a wancan jirgin mai dauke da be ran.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here