Wani magidanci na shirin gurfanar da matarsa a gaban kuliya sakamakon yi masa leƙen asiri a WhatsApp

0
2436

Wani mutum a Saudiyya na duba yiwuwar kai matarsa ƙara kotu saboda tana yi masa leƙen asiri kan saƙwanninsa na WhatsApp har tsawon wata tara.

Jaridar Saudi Gazette ta rawaito cewa mutumin ya gano matar tasa ne, wadda malamar makaranta ce, ta shiga WhatsApp ɗinsa sannan ta sauke dukkanin saƙwanninsa tare da hotuna da bidiyo ba tare da saninsa ba.

Mutumin ya bayyana abin da matar tasa ta aikata a matsayin leƙen asiri da kuma zamba ta intanet. Sai dai ya zaɓi a sasanta batun cikin lumana duk da girman laifin da aka aikata masa.

A gefe guda kuma, matar ta nemi ya sake ta sannan ta nemi ya fayyace kuɗaɗen tallafi da zai ba ta kafin karɓar takardar sakin.

A lokacin da Saudi Gazette ta tuntuɓi matar ba ta ce komai ba kan batun. Amma ta tabbatar da cewa ta nemi a raba auren saboda haka ba ta son ta bayyana sirrin aurensu a bainar jama’a.

A hannu guda kuma wata kwararriya kan harkar tsaron intanet ta yi gargadi kan amfani da Wi-Fi na kyauta da ake samu a filayen jiragen sama da otel-otel, inda ta bayyana su a matsayin wadanda za a iya yi wa mutum saurin kutse.

Bushra Al-Hout wacce manaja ce a wani kamfani ta shaida wa Saudi Gazette cewa manhajar Whatsapp na jawo hankalin masu kutse, kuma hadarin hakan na karuwa idan aka yi amfani da intanet a irin wuraren da aka lissafa a sama.

 

 

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here