Wanne hukuncin ne ya dace da Ibrahim Magu?

0
2516

Tsohon shugaban hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa wanda aka dakatar, Ibrahim Magu, ya musanta zarge-zargen da ake yi masa na wadaka da Naira biliyan 329 da hukumar ta gano an karkata su a kamfanin man kasar NNPC a lokacin da yake shugaba.

Ibrahim Magu ya ce sam shi ya maida biliyoyin cikin lalitar kamfanin bayan kwato su da ya yi daga hannun dillalan mai.

Bayan dakatar da shi da Shugaba Muhammadu buhari ya yi a ‘yan kwanakin da suka gabata, sai da aka tsare na kwanaki 10, kafin daga bisani aka sake shi.

Shin wani hukuncin ya cancanci Ibrahim Magu idan har aka same shi da laifi, ganin amanar da aka ba shi na kwato dukiyar kasa daga hannun wadanda suka karkata su?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here