Wata mata ta gurfana a gaban kotu saboda zargin yiwa ɗanta yankan rago

0
413

Babbar kotun jiha mai lamba 13 a jihar Kano, karkashin Justice Ibrahim Musa Karaye ta fara sauraron wata shari’a wadda gwamnatin jiha ta gurfanar da wata mata mai suna Saratu Ya’u.

Ana dai zargin Saratu Ya’u da laifin kashe dan ta na cikin ta ta hanyar yanka shi da wuka.

Kunshin zargin ya bayyana cewar Saratu ta yanka dan ta da wuka ta kuma yi tsirara tana rawa da wukar a hannunta.

Yayin da a ka karanta mata tuhumar ta amsa nan take lauyan gwamnati Lamido Abba Soron dinki ya roki kotun da ta yi umarnin a je gwada kwakwalwar matar domin tantance ko lafiyar ta kalau ko akasin hakan

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here