Ya kamata a wadata kowacce kasa da allurar riga-kafin corona – Buhari

0
100

Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi a samar da ingantacciyar allurar riga-kafin cutar Coronavirus ga dukkan jama’a ba tare da nuna son kai ba.

Shugaban dai ya nemi Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki matakin shawo kan annobar, ya ce kin yin hakan zai nuna gazawarta a cika muradun da aka gina majalisar a kai.

Kalaman Shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin, kasashen duniya masu karfin tattalin arziki ke samarwa kansu mafita ta hanyar kulla yarjejeniya da manyan kamfanonin sarrafa magunguna don wadata su da isassun allurar riga-kafin cutar ba tare da yin la’akari da kasashe matalauta ba.

Batun annobar Coronavirus da ta bulla a kasar Chaina a Disambar bara, ce dai ta mamaye babban taron Majalisar Dinkin Duniya na bana. Covid-19 ta janyo asarar rayuka kusan miliyan daya baya ga wasu sama da miliyan talatin da ta kama a sassan duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here