Ya kamata hukumar ƴan sanda ta rushe sashen anti – daba a Kano – Sha’aban Sharada

0
482

Shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilai Sha’aban Ibrahim Sharada ya buƙaci rundunar ƴan sandan jihar Kano da ta rushe sashin da ke yaki da ‘yan daba da ake kira ’Aniti-daba’.

Ɗan majalisar ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi bayan da ya ziyarci kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Habu Sani kan kisan da aka yiwa wasu matasa biyu a unguwar Sharada.

Idan za a iya tunawa a shekaran jiya Asabar ne ‘yan sandan Anti-daba suka kashe wasu matasa biyu, ‘yan ba ruwana a unugwar Sharada bayan da sukaje kamen masu laifi.

Matasan da suka hallaka a hannun ‘yan Anti-dabar sune Abubakar Isah da kuma Ibrahim Sulaiman da aka yi ittifakin abokanaine.

Wannance ta sanya al’ummar yankin na Sharada harzuka da kuma fara kiraye-kirayen a soke sashin na Anti-daba.

A cewarsu ko kadan ‘yan sandan na Anti-daba na wuce gona da iri a cikin ayyukan su.

Haka ta sanya Saha’aban Sharada kai koken sa ga kwamishi nan ‘yan sadan na jihar Kano kan daukar matakin gaggawa kan barnar da ‘yan sanda suka yi musamman ma na kashe yan baruwa na.

Cikin bukatar da dan majalisar ya gabatarwa kwamishina shi ne a hukunta wadanda suka yi barnar sannan a gyara musu ayyukan su ko kuma a rushesu ma  baki daya.

 

Kano Focus

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here