Ya kamata mulki ya koma Kudancin Najeriya a 2023 – El-Rufai

0
4460

Gwamnan jihar Kaduna ya nemi a miƙa wa yankin kudancin ƙasar nan mulki a shekarar 2023 bayan wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da BBC.

“Idan ka kalli yadda nake, ba na ɗaukar mutum yayi aiki tare da ni domin shiyyar da ya fito. Cancanta na ke dubawa, ina duba wanda idan aka ba shi amanar jama’a zai riƙe ta yadda ya kamata.”

Ya kuma ce, “A siyasar da ake yi a Najeriya, akwai tsarin da ake bi na karba-karba, inda kowa ya amince cewa idan arewa ta yi mulki shekara takwas, kudu za ta yi mulki shekara takwas.”

Ya ce duk da ba a rubuta tsarin karɓa-karɓan a tsarin mulki ba, amma kowane ɗan siyasa a ƙasar ya san da shi.

‘Shi yasa na fito na ce bayan Shugaba Buhari ya yi shekara takwas, ka da wani ɗan arewa ya nemi muƙamin. A bar ƴan kudu suma su sami shekara takwas.”

Da aka tambaye shi ko da gaske yana da ra’ayin tsayawa takarar shugabancin Najeriya, sai ya ce:

“Ana cewa ina son shugaban ƙasa tun ina ministan Abuja, amma ba na so. Wannan shirme ne.”

Ya kuma ci gaba da cewa Allah shi ke bayar da shugabanci, “ko kana so, ko ba ka so yana iya ba ka. Amma ni ban taɓa neman shugabancin Najeriya ba kuma babu wanda zai ce na taɓ a nema.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here