Yadda Ƴan mata 7 Suka mutu a wani shagon kitso a jihar Neja

0
966

Hukumomi a jihar Neja sun kaddamar da bincike don gano dalilin mutuwar wasu ‘yan mata guda 7 da sanyin safiyar ranar juma’a 31 ga watan Yuli, a daidai lokacin da ake shirin idin Babbar Sallah.

Wannan al’amari dai ya faru ne a garin Rijau da ke jihar Neja, bayanai sun nuna cewa ‘yan matan su 6 sun je wani shago ne da ake gyran gashi domin yin kitson sallah amma daga bisani sai dai aka ga gawarwakinsu tare da mai gyaran gashin. Uku daga cikin ‘yan matan daga iyali daya suka fito.

Shugaban karamar hukumar Rijau Honarabul Bello Bako, ya ce ya bada umurnin a yi wa yaran jana’iza kafin daga bisani a ci gaba da bincike, yayin da daya daga cikin iyayen yaran Alhaji Abdulrazak Rijau, ya ce iya abinda ya sani shi ne yaran sun tafi kitso, kawai sai dai aka kira shi aka fada masa abinda ya faru.

Rudunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da aukuwar lamarin inda kakakin ‘yan sandan jihar ASP Wasiu Abiodun ya ce suna kan binciken lamarin.

Gwamnatin jihar Neja, a ta bakin sakatarenta Ahmed Ibrahim Matane, ta bayyana lamarin a matsayin “mai tayar da hankali” ta kuma jajanta wa iyalan mamatan

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here